1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kisa kan wasu sojojin Sudan

Ramatu Garba Baba
August 6, 2021

Kotu a Sudan ta yanke wa sojojin da aka samu da laifin kisan masu zanga-zanga hukuncin kisa. Suna daga cikin dakarun RSF na hambararren shugaban kasar Oumar al-Bashir.

https://p.dw.com/p/3ydux
Sudan Khartum Abraq | Mitglieder der RSF - Rapid Support Forces
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Kotun da ke Khartoum ta yanke hukuncin kisa kan wasu dakarun Rapid Support Force(RSF) bayan da aka same su da laifin kisan masu zanga-zanga a lokacin da guguwar sauyi ta kada a kasar, shekaru biyun da suka gabata.

Alkalin kotun  Ahmed Hassan al-Rahma ya ce, ko kadan, bai dace a yi wa dalibai da suka fito zanga-zangar lumana irin wannan kisan gillar ba. Ya soki kisan da kuma ya ce, tsantsan rashin imani ne.

A shekarar 2019, zanga-zangar nuna adawa da mulkin Oumar al-Bashir ta barke saboda karancin abinci da man fetur a kasar. Kimanin mutane 128 alkaluma suka nunar sun mutu, daga kashe-kashen da aka zargi dakarun RSF da hambararren shugaban ya kafa a shekarar 2013 da aikatawwa. An dai nuna yadda aka yanke ta kafar talabijin din kasar.