1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomi a Jamus sun tashi tsaye domin shawo kan aƙidar Nazi

November 22, 2011

Ministan cikin gidan Jamus Hans-Peter Friedrich ya bukaci yin garanbawul ga hukumomin leken asirin ƙasa don magance masu aƙidar 'yan Nazi

https://p.dw.com/p/13Ehy
Ministan cikin gida na kasar Jamus Hans-Peter FriedrichHoto: picture alliance/dpa

'Yan siyasa a nan Jamus na cigaba da muhawara akan hanyoyin tsaro da kuma tattara bayanan sirri bayan da wasu gungun masu ra'ayin ƙyamar baƙi ta 'yan Nazi suka sulluɓe ba'a cafke su ba tsawon shekaru yayin da a waje guda kuma suka aikata kisan mutane goma ciki har da wata 'yar sanda. Da yake jawabi a wajen taro a birnin Berlin, Ministan cikin gida Hans-Peter Friedrich ya bada shawarar haɗe hukumomin leƙen asiri na cikin gida wuri guda, yana mai cewa an sami rarrabuwa a tsakanin waɗannan hukumi daga jiha zuwa jiha. Friedrich yace ko dai a rage yawan su ko kuma a haɗe ayyukan su wuri guda a ƙarƙashin hukuma ɗaya.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Usman Shehu Usman