1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Ba gaskiya a zargin corona da Amirka ke yi wa China

Binta Aliyu Zurmi
May 5, 2020

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta kamanta furcin da shugaban Amirkan ya yi a matsayin shaci fadi dangane da zargin da ya yi wa kasar China a kirkiro cutar covid 19.

https://p.dw.com/p/3bmHT
Tedros Adhanom Ghebreyesus Direktor WHO
Hoto: Getty Images/AFP

Hukumar ta ce babu wasu hujjoji kwakwara da ka iya tabbatar da zargi na cewar an kirkira cutar covid 19 a cikin dakunan harhada magunguna na garin Wuhan. Michael Ryan, shi ne daraktan kula da tsare-tsare na hukumar ta who yana mai cewa: "Ya ce mun saurari kwararru a kan sha'anin kimiya  a karo da dama wanda suka tantance kwayoyin cutar na covid 19 kuma suka tabbatar da cewar cutar ba  kirkirarta a ka yi ba don haka ba za mu taba yarda da wannan zargin ba".