1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HRW: Karuwar hare haren ta'addanci a yammacin Nijar

Abdourahamane Hassane
August 11, 2021

Kungiyar kare hakin Bil Adama, HRW ta bayyana fargaba kan karuwar hare-haren ta'addanci a yammacin Nijar inda tace daga watan Janairun 2021, kungiyoyi masu dauke da makamai sun kashe mutane 420 a Tillaberi da Tahoua

https://p.dw.com/p/3yrDK
Nigerianische Rebellen Niger Delta
Hoto: picture-alliance/AP Photo/G. Osodi

Kungiyar kare hakin Bil Adama ta Human Rights Watch ta bayyana fargaba a kan karuwar hare-haren ta'addanci a yammacin Nijar inda ta ce daga farkon watan Janairu na shekarar 2021 kawo yanzu, kungiyoyin da ke dauke da makamai masu jihadi sun kashe sama da mutane 420 a Jihar Tillaberi da Jihar Tahoua yayin da suka tilasta wa dubban jama'a yin kaura daga yankin. Kungiyar ta yi gargadin cewar alhaki ya rattaya a wuyan gwamnati na kare al'umma daga irin halin da aka shiga. Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wani rahoton da ta fitar. 

A cikin rahoton kungiyar ta Human Rights Wacht ta bayyana cewa shaidu sun bayyana wa wakilan su da suka gudanar da bincike a Jihar Tillaberi cewar 'yan tayar da tarzoma dauke da manyan makamai bisa babubura sun rika shiga kauyukan Tillaberi suna bi gida-gida suna kashe jama'aa farar hula mata da yara da tsoffi. Yayin da suke tare wasu a kan hanyar mota su tilasta musu fitowa kafin su harbe su har lahira. Rahoton ya ce daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su akwai hakimai da limamai da nakasassu da yara kanana wadanda sau tari ake kwacewa daga hannun iyayensu a kashe su.

Symbolbild | Niger Islamistischer Terrorismus
Shugaba Bazoum ke addu'a a kabarin sojojin Nijar da 'yan bindiga suka hallakaHoto: Boureima Hama/Getty Images

Wakilan na Human Rights Wacht sun je Nijar daga 23 ga watan Yuni zuwa 04 ga watan Yuli domin tattaunawa da shaidu a yankin na Tillaberi wadanda suka hada da sarakunan gargajiya da talakawa da Fulani da Bugaje da Zabarmawa da kuma hukumomin yanki a game da ta'asar da 'yan ta'addar ke yi a yankin na Tillaberi. Corine Dufka na cikin tawagar kuma ita ce Daraktar da ke kula da yankin Sahel a kungiyar Human Rights Wacht
''Musammun mun je har kauyukan da masu jihadin suka kai hare-hare, jama'a sun watse sun fice daga cikin kauyuka da dama saboda 'yan ta'addar tamkar suna yaki ne da farar hula su kashe jama'a su kone gari. Hakan ya saka jama'a cikin firgita da dimuwa wadanda sakamakon hare-haren suka rasa komai  su kan ficce su bar yankin.''

Rahoton ya ce a hare-hare guda tara na baya-bayan nan da 'yan ta'addar suka kai daga tsakiyyar watan Yuni zuwa karshen Yuli a garuruwa da kauyukan Tahoua da Tillaberi wadanda suka raba iyaka da Mali da Burkina Faso, sun aikata ta'addi mafi girma da su kan iya zaman laifukan yaki wanda kotun duniya za ta yi iya hukuntawa. Misali a hare-haren da aka kai a farkon watan Janairu a Tchomabangou da Zaroumdareye an kashe 'yan kabilar Zabarmawa 102 yayin da a cikin watan Maris da ya gabata a Jihar Tahoua masu jihadin suka kashe buzaye 170.

Symbolild Niger Islamistischer Terrorismus
Tawagar sojojin Nijar da ke fafatawa da 'yan ta'addaHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Tun a shekara ta 2015 'yan ta'addar masu alaka da kungiyar Al-kaida suka fara kai hare-hare a yamacin Nijar kan iyaka da Mali, A da suna kai farmaki ne kawai kan sojji da jami'an tsaro to amma daga bisani tun daga  2019 suka fara aikata kisa a kan farar hular, tare da kone makarantu Boko da shaguna da kantuna saboda jama'a na kin bin umarninsu na saka musu wasu dokoki na sharia na haramta shan taba ko giya ko sauraron kida ko ma haduwar mata da maza wuri daya, Corine Dufka ta ce akwai bukatar gwamnatin Nijar ta mayar da hankali wajen kare lafiyar al 'umma.

"Ta ce wannan al'amari na tayar da hankali wanda ya kamata a ce gwamnatin Nijar ta dauki karin matakai hakan ba zai yiwu ba sai ya kasance a cikin kasashen Mali da Burkina Faso da ke iyaka da Nijar suma sun kara karfafa matakan kare al'ummar su saboda 'ya ta'addar na kwararowa ne daga kasashen Mali da Burkina domin kawo hare-hare a cikin kauyukan Nijar na kan iyaka".

A karshe rahoton na Human Rights Wacht, ya nuna cewar al'ummar yankin yammacin kasar Nijar na Tillabery da Tahoua na fuskantar hali na tsaka mai wuya daga 'yan ta'addar da ke aikata kisa kan farar hula da ma sojojin gwamatin wadanda sau tari ke kashe farar hular kan cewar suna da hadin baki da 'yan ta'addar. Kawo yanzu dai tun daga shekara ta 2019 sama da mutane 4000 ne suka rasa rayukansu da suka hada da sojoji da farar hula a cikin hare-haren 'yan ta'adda a kasashen Nija da Mali da kuma Burkina Faso