1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin masu neman sauyi a Hong Kong

Abdourahamane Hassane
August 12, 2019

An ba da rahoton cewar hukumomi a Hong Kong sun soke tashi da saukar jiragen sama a filin saukar jiragen sama na yankin sakamakon mamaye filin saukar jiragen sama da masu zanga-zanga kusan dubu biyar suka yi.

https://p.dw.com/p/3NmA7
Hongkong Protest gegen China | Flughafen - Demonstration & Lahmlegung Flugverkehr
Hoto: Reuters/T. Siu

Masu boren da ke sanye da bakaken tufafi na yin wani gangami ne na fadikar da baki da ke shigowa bukatarsu na ganin an girka tsarin dimukaradiyya a yankin da ke a karkashin ikon China. Gwamnatin China uwargijiyar  ta Hong Kong  ta ce yunkurin na masu zanga- zangar da suka soma tun a cikin watan Yunin da ya gabata domin neman  yancin gishin kai, da tsarin dimukaradiyya na kama da ta'addanci.