1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyamar mika masu aikata laifi a China na kamari a Hong Kong

Abdoulaye Mamane Amadou
July 9, 2019

Hukumomi a yankin Hong Kong sun bayyana mutuwar dokar nan da ke sallama wadanda suka aikata laifi ga kasar China a daidai lokacin da masu bore da kyamar dokar ke ci gaba da kara matsin lamba ga gwamnati.

https://p.dw.com/p/3LmGf
Hongkong PK Carrie Lam
Hoto: picture-alliance/AP Photo/V. Yu

Shugabar gwamnatin yankin Hong Kong Carrie Lam ta bayyana a wannan Talatar da cewa kudirin dokar nan da aka shigar gaban majalisa da ya janyo da kazamar zanga-zanga ya mutu murus.

Sai dai masu aiko da rahotanni sun ce Carrie Lam, ba ta fito fili ta yi bahasi kan ko janye dokar ne aka yi kwata-kwata ba, batun da kuma ya kara haifar da fargaba da ma harzuka masu zanga-zangar da ke nuna kyama game da dokar.

A yayin wani taron manema labarun da ta jagoranta Missis Lam ta ce a shirye ta ke da ta gana da kungiyar daliban kasar da ke boren a bainar jama'a ba tare da gindaya wani sharadi ba, batun da kuma masu zanga-zangar suka yi watsi da shi tare da kiran wani sabon gangami.