1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Kasar Chadi a mutu

Abdourahamane Hassane
August 24, 2021

Tsohon shugaban Kasar Chadi Hissen Habre wanda wata kotu a Senegal ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai ya mutu a gidan yari.

https://p.dw.com/p/3zQY3
Hissene Habre
Hoto: picture-alliance/dpa

Hissen Habre wanda a shekara ta 2016 wata kotu a Senegal ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai bisa zargi aikaita gisan gilla da cin zarafin bil Adama a zamanin mulkinsa ya mutu yana da shekaru 79: Ya dai gudanar da mulki daga shekara ta 1982 zuwa 1990 kafin marigayi Idriss Deby ya kifar da gwmnatina  abin da ya sa ya tsere zuwa gudun hijira a Senegal. Daga bisani kungiyoyin kare hakkin bil Adama na kasa da kasa su shigar da kara na zarginsa da laifukan kisa na jama'a da azabtarwa da fyade a wata kotun a Senegal.