1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hillary Clinton ta kawo ƙarshen rangadin Gabas Ta Tsakiya

July 16, 2012

Clinton ta tattauna da mahukuntan Isra'ila da na Falasɗinu a kan shirin zaman lafiyar yankin Gabas Ta Tsakiya da ya cije.

https://p.dw.com/p/15Ygi
Israel's President Shimon Peres (L) stands with U.S. Secretary of State Hillary Clinton before their meeting in Jerusalem July 16, 2012. Clinton and Israeli officials will discuss on Monday Egypt's political upheaval, Iran's nuclear program and the stymied Israeli-Palestinian peace process. REUTERS/Ronen Zvulun (JERUSALEM - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta ce guguwar canji dake kaɗawa a ƙasashen Larabawa ta kasance wata damar samun daidaituwar al'amura, zaman lafiya da kuma Demokraɗiyya a yankin Gabas Ta Tsakiya. Bayan tattaunawa da ta yi da shugaban Isra'ila Shimon Peres a Birbnin Ƙudus, Clinton ta ce mummunan rikicin da ake yi a Siriya da taƙaddamar nukiliya da Iran suna taka rawa bisa wannan manufa. Ta ce ko da yake wannan lokaci ne na rashin sanin tabbas amma kuma yana tattare da damarmaki.

"Wata dama ce ta inganta burin tabbatar da tsaro, kwanciyar hankali, zaman lafiya, demokraɗiyya haɗe da wadatar arziki ga miliyoyin mutane a wannan yanki."

A shawarwari da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da firaministan Falasɗinawa Salam Fayyad, sakatariyar harkokin wajen ta Amirka ta yi ƙoƙarin ganin an samu wani ci-gaba a shirin zaman lafyia tsakanin Isra'ila da Falasɗinu wanda ke kwan gaba kwan baya tun wasu shekaru da suka gabata. Isra'ila ce matakin ƙarshe na rangadin kwanaki 12 da Clinton ta kai a wasu ƙasashen yankin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu