1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hillary Clinton ta gana da Hussain Tantawi

July 15, 2012

Amirka ta bukaci shugabannin Masar da su karfafa demokradiyyar kasar

https://p.dw.com/p/15Y9M
Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service Egyptian military chief Field Marshal Mohamed Hussein Tantawi (L) shakes hand with U.S. Secretary of State Hillary Clinton before their meeting at the Defence Ministry in Cairo July 15, 2012. Hundreds of people chanted anti-U.S. and anti-Islamist slogans outside Clinton's hotel on Saturday as the U.S. secretary of state urged Egypt's military and Muslim Brotherhood to complete a transition to full democratic rule. REUTERS/U.S Embassy Media Office/Handout (EGYPT - Tags: POLITICS MILITARY) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

A ci gaba da ziyarar da take yi a kasar Masar sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta gana da shugaban rundunar sojin kasar, Field Marshal Hussain Tantawi inda ta yi kira gareshi da mukarrabansa da su dafa wajen ganin tsarin demokradiyyar kasar ya samu gindin zama. Uwargida Hillary ta ce hakan zai taimaka wajen ciyar ta kasar gaba musamman ma dai ta bangaren tattalin arziki. Baya ga haka ta kuma gana da wakilan Kiristoci Kibdawa na kasar ta Masar inda ta jaddada kudurin Amirka na kare hakkin dukannin al'ummar kasar: Maza da Mata, Musulmi da Kiristoci baki daya.

Ziyarar ta Uwargida Hillary wadda ke karewa a yau na zuwa ne daidai lokacin da ake sa in sa tsakanin sabon shugaban kasar Muhammad Mursi na jam'iyyar 'Yanuwa Musulmi da kuma jagoran majalisar kolin sojin kasar Field Marshal Hussain Tantawi musamman ma dai batun jan ragamar madafun ikon kasar.

Mawallafi. Ahmed Salisu
Edita: Halima Balaraba Abbas