1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hillary Clinton na ziyara a Masar

July 14, 2012

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta isa birnin Alƙahiran Masar a asabar ɗin nan inda ta ke wata ziyara ta kwanaki biyu don tallafawa ƙasar ta Masar daidaita tsarin demokraɗiyarta.

https://p.dw.com/p/15Xtb
Hoto: dapd

Ya yin wannan ziyarar, Uwargida Hillary ta gana da shugaban ƙasar Muhammad Mursi da kuma shugaban majalisar ƙolin sojojin Masar ɗin Field Marshal Hussein Tantawi.

Yayin ganawar da su ka yi sakatariyar harkokin wajen Amurkan ta tabbatarwa da Shugaba Mursi cikakken goyon bayan Amurka musamman ta ɓangare mulkin farar hula.

Masu aiko da rahotanni dai sun bayyana cewar yayin ziyarar, sakatariyar harkokin wajen Amurkan za ta kuma gana da ƙungiyoyin mata da kuma kiristoci kiɓɗawa.

Ziyarar ta ta ta kwanaki biyu dai za ta su maida hankali wajen tattaunawa kan tsarin mulkin ƙasar da sha'anin da ya danganci majalisar dokokin ƙasar da ma dai sauran bangarori da za su taimaka wajen tabbatar da ɗorewar tsarin demokraɗiyya.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Abdullahi Tanko Bala