1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai sauya rigunan kujerun mota

April 1, 2020

Wani matashi a jihar Kadunan Najeriya, na yin sana'ar dinka rigunan kujerar mota daga yadi zuwa leather ko daga leather zuwa yadi. Matashin na zaune a Sabongarin Tudunwada a Kargi Road da ke Sabongarin a Kaduna ta Kudu.

https://p.dw.com/p/3aJAA
Screenshot DW Video HdM: Kaduna Autositz Schneider
Matashi mai gyaran kujerun mota a jihar Kaduna da ke Najeriya

Matashin mai suna Mohammed Ibrahim na da shekaru 22 a duniya kuma a yanzu haka yana karatun HND akwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kadunan. Matashin dai ya kwashe kusan shekaru uku yana gudanar da sana'ar sauya rigunan kujerun motar, koda yake sana'ar dinkin rigunan kujerun motar da sauya su na bukatar nutsuwa da jajircewa  da kuma kwarewa kana sana'a ce wadda ba kasafai mutane kan yi ta ba.

Akan bukaci sauya rigunan kujerun motar wani lokaci idan sun tsufa ko kuma idan na yadi ne a mayar da su na fata. Sau da dama akan yi kicibis da kalubale musamman ma a sana'o'in hannu, a cewar Ibrahim batun da ya shafi kayan aiki sakamakon rufe kan iyaka da aka yi, ya zame masa kalubale na wani lokaci saboda gum din da suke amfani da shi sai an shigo da shi daga waje. Sai dai duk da kalubalen da yake fuskanta, ya ce a gefe guda akwai nasarori daya samu cikin wannan sana'a