1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Öl Spekulation

Tijani LawalFebruary 3, 2011

A halin da ake ciki yanzu haka farashin ɗanyyun kayayyaki sai daɗa hauhawa yake yi, musamman ma man fetir, lamarin da ka iya zama barazana ga farfaɗowar al'amuran tattalin arziƙin da ake samu.

https://p.dw.com/p/10APA
Al'amura sai daɗa yin tsamari suke a ƙasar MasarHoto: dapd

Kazalika wannan ci gaba na ɗaukar hankalin 'yan baranda da ma 'yan kasuwa, waɗanda a sakamakon take-takensu farashin ɗanyyun kayayyakin zai ƙara haurawa sama. Ummalaba'isin hakan kuwa shi ne tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a Masar da sauran ƙasashen Larabawa.

Iran Benzin Rationierung
Duk mai jan mota yana jinta a jika in ya je shan maiHoto: ISNA

Duk dai mai jan mota yana jinta a jika idan ya je shan mai. Domin kuwa tun abin da ya kama daga farkon watan janairun da ya wuce farashin man ke tashin gwaron zabo. A kuma halin da ake ciki yanzu farashin ɗanyen mai da ake haƙa a North Sea ya kai dalar Amirka ɗari kuɗin ganga guda. Galibi 'yan kasuwa na ɗora laifin ne akan yamutsin da ake fama da shi a ƙasar Masar. Domin kuwa ko da yake ƙasar ba ta da arziƙin mai, amma ita ce ke da ikon mashigin Suez, wanda ta kansa ne ake jigilar man zuwa Turai. An saurara daga Carsten Fritsch, ƙwararren masani akan al'amuran ɗanyyun kayayyaki a bankin kasuwanci na Commerzbank dake Frankfurt yana mai cewar:

"Abin da ake fargaba shi ne ka da tashin-tashinar ta Masar ta kai gurgunta wannan muhimmiyar hanya da ma sauran bututan da ake amfani dasu bisa manufa. A baya ga haka akwai fargaba game da yiwuwar yaɗuwar tashin-tashinar zuwa ƙasashe masu arziƙin mai kamar Aljeriya ko Libiya. Hakan zata yi mummunan tasiri akan cinikin man."

To sai dai kuma bisa ga dukkan alamu ba mawuyacin halin da ake ciki a ƙasar Masar ne kaɗai dalilin tashin farashin man ba, kazalika su ma 'yan baranda suna da hannunsu a wannan ci gaba.

"Suna amfani da mawuyacin halin da ake ciki don ƙara tsawwala farashin. To sai dai kuma abin lura shi ne akwai kasada a kasuwar ma gaba ɗaya ta yadda ba za a ba wa rawar da 'yan barandan ke takawa wani muhimmanci ba."

To ko shin wata barazana ce ta ɓillar wani sabon rikici na mai ke neman kunno kai? Carsten Fritsch cewa yayi:

"A dai halin da ake ciki yanzu akwai adanin mai mai yawan gaske da aka tanadar a rumbuna a sassa daban-daban na duniya kuma ƙungiyar OPEC na da ikon bunƙasa yawan mai da ƙasashenta ke haƙowa idan zarafi ya kama, a saboda haka muke tattare da imanin cewar farashin zai sake yi ƙasa da dolar Amirka ɗari nan gaba."

A haƙiƙa dai ba wanda zai iya iyin hasashen yadda farashin zai kaya. Amma ala-kulli halin ɓangaren cinikin mai na samun bunƙasa kuma kamfanonin makamashi na samun ƙazamar riba, lamarin da masu motoci ke jinta a jika. Sai dai kuma ko ba daɗe ko ba-jima za a kai maƙura, inda tsadar zata yi tasiri akan sauran kayan buƙatu na yau da kullum. Ta haka murna zata sake komawa ciki dangane da sararawar da aka fara samu ga tattalin arziƙin duniya.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Abdullahi Tanko Bala