1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hauhawar farashin ɗanyen mai sakamakon halin da ake ciki a Najeriya da Iran

January 12, 2012

Farashin ɗanyen mai ya ƙaru da kusan dala guda a Amirka da Asiya, biyowa bayan barazanar da ƙungiyar Pengason ta yi na dakatar da haƙon mai a najeriya, da kuma takun saka da Iran ta ke yi da manyan ƙasashen duniya.

https://p.dw.com/p/13iVb
Haihauwar farashin ɗanyen man ta shafi Kasuwar New york na Amirka
Haihauwar farashin ɗanyen man ta shafi Kasuwar New york na AmirkaHoto: picture-alliance/dpa

Farashin ɗanyen man fetur ya tashi a kasuwannin duniya sakamakon fargaba da ake nunawa dangane da zanga-zangar da ta biyo bayan janye tallafin mai a Tarayyar Najeriya, da kuma neman haramta wa Iran fitar da man da ta ke haƙowa. A Kasuwar birnin New York na ƙasar Amirka dai, ana sayar da ganga ɗaya akan dallar Amirka 101 da kuma centi 78. Ma'ana an sami ƙarin centi 91 akan kowace ganga. A kasuwannin nahiyar Asiya ma, an samu ƙarin kusan dala ɗaya akan wace ganga na ɗanyen mai.

Wannan haihawar farashin na da danganta da niyar ƙungiyar gammayar Turai na ƙaƙaba wa man Iran takunkumi, da nufin nuna rashin amincewarta da shirin teheran na bunƙasa Uranium. Ita kuwa Japan ta yi alƙawarin rage soyo mai daga ƙasar ta Iran. A Najeriya kuwa, ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ma'aikatan man fetur ta yi barazanar dakatar da hakon man daga ranar lahadi mai zuwa, idan gwamnati ba ta mayar da tallafin da ta janye na man fetur ba. A halin yanzu dai shugaban Gudluck Jonathan na ganawa da shugabannin ƙungiyoyin kodagon da nufin fahimtar juna game da yajin aiki na sai baba ta gani.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar