1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hatsarin nukiliya a Japan

March 14, 2011

Ana ƙara samun fargaba kan halin da tashoshin nukiliyar Japan ke ciki bayan masifar tsunami da ta aukawa ƙasar.

https://p.dw.com/p/10Yr6
Jami'an tsaro a japan ke aikin ƙaurar da mutane kusa da tashar nukiliyaHoto: picture-alliance/dpa

A ƙasar Japan ana ƙara samun tukwanen dafa makashin nukiliya dake facewa, sakamakon rashin aikin na'urorin san'ya'ya makashin. Tun da fari dai tukwanen sarrafa makashin biyu sun samu irin wannan matsalar kafin wanda ya faru a yau. Yanzu haka dai masana a kasar ta Japan suna kai kawo don hana sauran tukwanen da ke sarrafa makashin daga samun matsalar da za ta kai su ga facewa. Wani jami'in gwamnatin ƙasar ya sanar da cewa kawo yanzu dai babbar na'urar dake sarrafa makashin babu abinda ya taɓa ta. A kalla mutane tara suka samu rauni bayan facewar da aka yi. A ƙasar ta Japan dai yanzu katsewar wutar lantarki, ta sa aƙalla gidaje dubu 330 cikin duhu, ciki kuwa har da wani ɓangaren birnin Tokyo. Kazalika ƙarancin ruwa da abinci, shima yana shafar miliyoyin mutane yanzu haka. Firai ministan ƙasar yace yawan waɗanda suka mutu zai zarce yadda aka gyasta da fari na mutane dubu goma, inda a yau kaɗai aka tsinci gawaki 2000 a gabar teku.

Darasi ga sauran ƙasashe


Matsalar da ta faru da tashoshin nukilya a ƙasar ta Japan ya jawo mahawara a ƙasar Jamus. Ministan harkokin wajen ƙasar Guido Westerwelle yace gwamnatin ƙasar za ta sake shawara, a kan batun ƙara wa'adin da aka yi na rufe tashoshin nukilyan kasar 17. Kwamishinan makashi na Tarayyar Turai Günther Öttinger yace kamata ya yi a binciki tsofaffen tashoshin nukiyar ƙasar Jamus. Kazalika ministan kare mahalli na ƙasar ta Jamus Norbert Röttgen, yace dole a binciki matakan kariya dake cikin tashoshin nukiliyar kasar. Shi kuwa shugaban babbar jam'iyar adawan kasar ta Social Demokrat, Sigmer Gabriel ya buƙaci da a rufe tsoffin tashoshin nukiliyar ƙasar ta Jamus nan take.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Mohammed Abubakar