1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin 'yan tawayen Mao a Indiya ya hallaka 24

May 26, 2013

Ƙungiyar tawayen Mao ta fara adawa da gwamnatin Indiya tun shekarar 1967, inda ta ce tana gwagwarmayar samarwa 'yan ƙasa ayyukan yi ta kuma girka tsarin Kommunisanci.

https://p.dw.com/p/18eIk
Indian Prime Minister Manmohan Singh, blue turban, talks to Congress party president Sonia Gandhi, at a function to mark the completion of three years of the government in New Delhi, India, Tuesday, May 22, 2012. (Foto:Manish Swarup/AP/dapd)
Firaminista Manmohan Singh da shugabar jamiyyarsu ta Congress Sonia GandhiHoto: dapd

'Yan sanda a Indiya sun ce 'yan tawayen Mao wajen su 300 waɗanda kuma suka yi ɗammara da manyan makamai sun hallaka aƙalla mutane 24 bayan da suka kai hari kan wani ayarin motocin da ke ɗauke da shugabanni da magoya bayan Jamiyyar Congress a matakin ƙaramar hukuma, a ɗaya daga cikin jihohin da ke tsakiyar Indiya.

Wannan harin shine mafi muni a tsukin shekaru uku, kuma na baya-bayan nan a taƙaddamar da ke tsakanin ƙungiyar tawayen da hukumomin ƙasar.

Shugabar Jamiyyar Sonia Gandhi wadda ta ruga Jihar da wannan bala'in ya afku tare da shugaban ƙasa Mahmohan Singh sun yi allah wadai da harin, wanda aka ce wasu 37 sun yi mummunar rauni kuma suna karɓar magunguna a asibiti.

Ga dai shaidar da wani wanda ya ganewa idanunsa yadda wannan hari ya afku ya bayar

"'Yan tawayen sun tsayar da mu suka fara kai mana hari, sai shugaban jamiyyar mu ya sauko daga na sa motar ya roƙe su ya ce kada su kashe kowa banda shi, sai suka harbe shi da harsasai sun kai ɗari sanan daga ƙarshe suka harbe shi da dutse a goshi"

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman