'Yan ta'adda sun hallaka sojojin Burkina Faso
May 12, 2020Talla
Rahotanni daga Kankanfogouol da ke arewacin Burkina Faso sun yi nuni da cewa kimanin sojojin kasar hudu ne suka halaka a yayin da wasu kuma hudun suka yi batan dabo sakamakon wani harin kwantar bauna da mayakan jihadi suka yi wa ayarin sojan kasar da ke sintiri a yankin da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Wata majiyar tsaron kasar ta tabbatar da harin tare da bayyana cewa tuni dakarun rundunar sojan kundun balar kasar ta kaddamar da wani samame domin kakkabe mayakan da suka kai harin.
Ba tun yau ba dai kungiyoyi masu tayar da kayar baya ke labawa da yankin suna kai hare-haren ta'addanci a tsakanin kasashen biyu na Nijar da Burkina Faso.