1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari a Yemen

December 31, 2020

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da ya hallaka mutane 26 a Yemen.

https://p.dw.com/p/3nOox
Jemen l Explosion am Flughafen in Aden
Hoto: Fawaz Salman/REUTERS

Kimanin mutane 26 suka hallaka, yayin da wasu sama da 50 suka sami mummunan rauni a wani harin ta'adanci da aka kai a filin jirgin sama na Aden da ke Yemen. Harin da aka kaiwa manyan jami'an gwamnatin hadin kai na Yemen din da suka hada da ministoci da wasu masu mukami a gwamnatin, wanda kamfanin dillacin labarai na AFP ya ce babu ministan da abin ya rutsa da shi. Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ya yi tir da hari, kuma ya bayyana shi da maida hannun agogo baya a kokarin samar da zaman lafiya da ake yi a kasar.n An dai dora alhakin harin ne  a kan mayakan Huthis da ke samun goyon bayan Iran.