1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Harin ta'addanci a kasar Mali ya hallaka mutane 40

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 3, 2024

Harin ya faru a yankin Mopti a daidai lokacin da ake tsaka da gudanar da biki

https://p.dw.com/p/4hndy
Hoto: MICHELE CATTANI/AFP/Getty Images

Wani harin ta'addanci a arewacin kasar Mali ya hallaka mutane 40, kamar yadda magajin garin  Bankass Moulaye Guindoin ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Reuters ta wayar tarho.

Karin bayani:Mali: 'Yan bindiga sun kashe mutane a Mopti

Harin ya faru a kauyen Djiguibombo na yankin Mopti mai fama da hare-haren 'yan ta'adda masu alaka da al Qaeda da IS, a daidai lokacin da ake tsaka da gudanar da biki, kuma yawancin mamatan maza ne.

Karin bayani:MDD na fargabar fantsamar rikicin kasashen Sahel zuwa makwabta

Dubban mutane ne dai suka rasa rayukansu tun bayan barkewar tashe-tashen hankula a kasashen yankin Sahel, da suka hada da Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar, wanda ya janyo juyin mulkin sojoji a kasashen.