1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ta'adanci a Burkina Faso

Binta Aliyu Zurmi
December 2, 2019

Jami'an tsaro sun kaddamar da bincike a kan mummunan harin da aka kai a kan wasu al'umma mabiya addinin kirista wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha hudu tare da jikata wasu.

https://p.dw.com/p/3U79C
Burkina Faso Messe in einer katholischen Kirche in Ouagadougou
Hoto: Imago Images/UIG/P. Lissac

A wata sanarwar da gwamnan yankin da abun ya faru ya fitar, ya yi Allah wadai da harin inda ya kuma kara da cewar al'ummar yankin da su tashi tsaye don lura da ire-iren mutanen da ke kai kawo a yankin. 

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin wannan harin. Amma ana zargin mayakan jihadi da suka yi kaurin suna a kai hare-haren ta'addanci a kasar da hannu a harin.