1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a tashar jiragen ruwan Odesa

Binta Aliyu Zurmi
September 3, 2023

Hukumomi a birnin Kyiv da safiyar wannan rana ta Lahadi sun sanar da wani mumunan hari na jirage marasa matuka akalla 25 da aka kai wa birnin Odesa mai tashar jiragen ruwa a kudancin Ukraine.

https://p.dw.com/p/4VtIJ
Ukraine-Krieg | Russicher Angriff auf Getreidespeicher in Odessa
Hoto: Odesa Regional Administration Press Office/AP/dpa/picture alliance

Harin na wannan safiyar ya lalata kayayaki da dama a wasu tashoshin ruwa tare kuma da jikkata fararen hula mutum biyu.

Rundunar sojin sama ta Ukraine ta ce harin da ya kwashe sama da sa'o'i uku, ta yi nasarar harbo jirage 22 kirar samfurin kasar Iran.

Birnin Odesa na daga cikin birane Ukraine da ya jima yana fuskantar barazanar hari daga Rasha, kuma ko baya ga zama guda daga cikin manyan tashoshin ruwan Ukraine da ake fitar da hatsi, ya kuma kasance wajen da 'yan yawon bude ido ke ziyara don tarihinsa.

A farkon shekarar na hukumar kula da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta baiyana Odesa a matsayin birnin tarihi na duniya da ke fuskantar hadari.