1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya yi ɓarna a Somaliya

October 4, 2011

Wani tashin bam ya hallaka mutane da dama a ƙasar Somaliya wanda yaƙi ya ɗai-ɗai ta, inda aka kia harin a birnin Mogadishu a tsakiyar mutane

https://p.dw.com/p/12ldB
Motar da aka kai hari da ita yau a MogadishuHoto: picture-alliance/dpa

A ƙasar Somaliya masu tada ƙayar baya sun kai harin bam, inda aƙalla mutane 70 suka hallaka wasu dadama suka jikkata, harin ya zo ne bayan makwanin da aka samu ana zaman lafiya a birnin. An dai kai farmakin a harabar ma'aikatar tsaron ƙasar dai-dai lokacin da mutane ke kai kawo. Wannan harin dai shine mafi ɗaukar rayuka da aka samu a ƙasar da yaƙin ya ɗai-daita a bana.

Somalia Mogadischu
Sheik Ali Mohamud Rage, kakakin ƙungiyar Al-ShababHoto: AP

Maharin dai ya nufi shiga da motar da ya maƙare da bama-bamai izuwa cikin ginin ma'aikatar ilimi, amma da jami'an tsaro masu bincike a shingayen bince suka tsaida shi don bincike sai ya tada bama baman, inda nan take wurin tirniƙe da yahaƙi, motoci da gine-gine dake kusa da wurin suka kama da wuta. An ga jami'an tsaro na zaƙulu waɗanda suka jikkata. Ali Musa shine babban jami'in agajin gaggawa a Mogadishu, ya kuma shaida wa kamfanin dillalcin labarai na AFP cewa, aƙalla mutane 70 sun mutu wasu sama da 42 sun jikkata.

Islamistische Rebellen in Somalia
Dakarun ƙungiyar Al-ShababHoto: AP

Kamar yadda aka saba ƙungiyar dake tada ƙayar baya a ƙasar ta tsagerun Al-Shabab, jim kaɗan sai ta fito ta ɗauki alhakin kai harin. Wannan shine tashin hankalin da aka gani tun watan Augosta da ƙungiyar Alshabab ta janye daga birnin Mogadishu bisa koransu da dakarun kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka suka yi. Da ma dai an yi zaton cewa ƙungiyar za ta ƙaddamar da yaƙin sunƙuru, tun bayan da aka koresu da ƙarfin tsiya daga birnin, kuma a 'yan makwannin nan an gano bama bamai da yawa kafin facewarsu wasu kuwa suna facewa kafin a isa inda aka nufa da kai su.

Kafin shekara ta 2007 bakwai a lokacin da Amirka da haɗin gwiwar ƙasar Habasha suka tunɓuke gwamnatin Somalaiya da Sharif Ahmed ke jagoranta, ba a jin tashin bam a birnin Mogadishu. Amma tun wannan lokacin harin bama bamai ya zama ruwan dare.

Ƙungiyar Al-Shabab na alaƙa da Alƙa'ida kuma a yanzu ƙungiyar na ƙara samun gindin zama a kusuruwar gabacin Afirka. Ƙungiyar Al-shab dai regowar mayaƙan Afganistan da Iraƙi ne, inda jami'an ta suka samu horon haɗa bama-bamai da kuma ƙurewa wajen kai harin sari ka noƙe.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi