Harin bam ya sake salwantar da rayuka a Siriya
March 18, 2012Gidan talibijin na kasar Siriya ya rawaito cewa wata karamar mota dankare da bama-bamai ta fashe a wata unguwa da ke birnin Aleppo a wannan lahadin, wuni guda bayan da wasu tagwayen bama-bamai suka fashe a babban birnin kasar wato Damascus.
Majiyoyin adawa sun ce harin ya shafi wani yanki da ke kusa da wani ofishin jami'an tsaro. Wakilan kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch wadanda ke sanya ido a yadda alamaura ke gudana a Siriyar sun ce harin ya salwantar da rayuka kuma da dama sun yi rauni, to sai dai basu bada adadin wadanda abun ya shafa ba. Harin na ranar lahadi, shine harin kunar bakin wake na biyar, wanda aka kai a karamar mota tun bayan da aka fara nuna adawa da mulkin shugaba Bashar Al-Assad na tsawon shekara guda yanzu.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar