1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari kan motar safa a Siriya

Suleiman Babayo MAB
October 20, 2021

Hari bam kan motar safa ta sojoji ya halaka mutane 14 yayin da wasu da dama suka jikata a birnin Damuscus na kasar Siriya.

https://p.dw.com/p/41tdF
Syrien Damaskus | Bombenanschlag auf Bus
Hoto: FIRAS MAKDESI/REUTERS

Rahotanni daga kasar Siriya sun nuna cewa mutane da halaka kana wasu sun samu raunika lokacin da bam ya fashe da ake harin motar safa ta sojoji a birnin Damascus fadar gwamnatin kasar.

Tashar talabin ta kasar ta ce lamarin na safiyar wannan Laraba ya faru lokacin da aka ji karar fashewar abubuwa guda biyu.

Wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa kimanin mutane dubu-350 suka halaka sakamakon yakin basasa da ke faruwa a kasar a shekaru 10 da suka gabata, abin da ya samo asali bisa zanga-zangar neman kawo karshen gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta kasar ta Siriya.