1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari ya salwantar da rayuka a Burkina Faso

Mouhamadou Awal Balarabe
August 8, 2020

Akalla mutane 20 sun rasa rayukansu a harin da 'yan bindiga suka kai a wata kasuwa da ke gabashin kasar Burkina Faso. Dama yanki na sahun gaba na wadanda suke fama da ayyukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/3geEX
Burkina Faso Ouagadougou Explosionen
Hoto: Getty Images/AFP/A. Ouoba

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe mutane 20 tare da jikkata da wasu  da dama, a lokacin da suka kai hari a wata kasuwa da ke garin Namougou a gabashin Burkina Faso. Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa  maharan sun afka cikin kasuwar kan babura, sannan suka bude wuta a daidai lokacin da ake tsaka da cin kasuwa a ranar Jumma'a.

Gwamnan yanki gabashin Burkina Faso Kanal Saidou Sanou ya ce ana farautar wadanda  suka kai wannan harin, sannan yan yii kira ga jama'a da  "su yi taka tsantsan tare da ba da hadin kai ga jami'an tsaro da ke gudanar da bincike". Wannan mummunan harin dai ya yi kama da wanda ya faru a kasuwar shanu ta Kompienbiga, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 30 a karshen wata Mayu a gabashin kasar.

Gabashi da Arewacin Burkina Faso su kasance yankuna biyu da matsalar ta’addanci ta fi shafa, wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,100 yayin da sama da mutane miliyan guda suka yi gudun hijira cikin shekaru biyar da suka gabata.