1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 60 sun halaka samakaon hari a Jamhuriyar Nijar

March 17, 2021

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ware kwanaki uku domin zaman makokin wani harin ta'adancin da ya rutsa da 'yan kasar kusan 60.

https://p.dw.com/p/3qj24
Niger Agadez Wrack eines Selbstmordattentats
Hoto: AFP/B. Hama

Mahukunta a jamhuriyar Nijar sun tabbatar da kisan wasu 'yan kasar kusan 60 bayan da wani harin 'yan ta'adda da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai kan wasu yan kasuwa.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar Abdourahmane Zakaria wanda shi ne ya tabbata da afkuwar lamarin da kuma kididdigar adadin wadanda suka rasa rayukansu a gidan talabijin na kasar, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a kasar ta Nijar.

Yan kasuwar dai sun hadu da ajalinsu ne a lokacin da suke dawo wa daga cin wata kasuwar dabbobi ta Banibangou a yankin Tllaberi da ke makwabataka da kasashen Mali da Burkina Faso.