1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kara samun hare-hare a Mali

January 24, 2021

Tagwayen hare-haren mayakan jihadi a Mali sun kashe dakarun kasar 6 artabu lokacin da sojojin suka amyar da wuta.

https://p.dw.com/p/3oM7c
Mali Fana | Soldat | Sicherheit in Mail
Hoto: Getty Images/AFP/M. Cattani

Rundunar sojin Mali ta tabbatar da adadin  jami'an sojinta da suka mutu a wani tagwayen harin da aka kai a daren jiya sun kai 6 yayin aka ga gawawwakin wasu 30 da ake zargin mayakan jihadi ne.

Harin dai ya auku ne kusa da iyaka da kasar Burkina Faso, kuma tuni aka kwashe sauran dakarun wadanda suka ji rauni.

Ko a watan Satumbar shekarar 2019 an kai wani hari sansanin dakarun da ke zama mafi munin hare-hare da aka kai Mali tun shekarar 2012, inda sojoji 50 suka rasa rayukansu.