1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsageru sun halaka mutane 13 a kasar Burkina Faso

Suleiman Babayo ZMA
August 5, 2022

A kasar Burkina Faso wani harin tsageru masu kaifin kishin Islama ya halaka mutane 13 da suka hada da jami'an tsaro hudu.

https://p.dw.com/p/4FCEA
Benin | Fotoreportage Marco Simoncelli aus Porga
Hoto: Marco Simoncelli/DW

Tsageru masu kaifin kishin addinin Islama dauke da makamai sun halaka sojojin Burkina Faso hudu da fararen hula guda tara a wani harin kwanton bauna a yankin arewacin kasar. Wata sanarwa ta rundunar sojan kasar ta ce lamarin ya faru a wannan Alhamis da ta gabata.

Fararen hular da harin ya ritsa da su na cikin tawogar mayakan sa-kai da ke taimakon sojojin yaki da tsageru.

Tuni sojoji suka mayar da martani tare da halaka mutane 34.

Ita dai kasar Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka tana kasance tana fuskantar hare-hare kungiyoyin Musulmai masu ikirarin jihadi na Al-Ka'ida da IS tun shekara ta 2015.

A watan Janairu sojoji sun kwace madafun iko domin magance matsalar, amma tana ci gaba da faruwa a yankin arewacin kasar.