1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan bindiga ya halaka 'yan sanda a Tanzaniya

Ramatu Garba Baba
August 25, 2021

Yan sanda uku da wani farar hula na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon wani hari da wani dan bindiga ya kai a kusa da ofishin jakadancin Faransa da ke Dar es Salaam.

https://p.dw.com/p/3zTrB
Iran Abdullah Ahmed Abdullah Al-Qaidas Nummer zwei getötet | Anschlag in Dar es Salaam
A shekarar 1998 an kai munmunan harin ta'addanci a TanzaniyaHoto: AMR NABIL/AFP

Rundunar 'yan sanda Dar es Salaam, babban birnin kasar ta Tanzaniya, ta tabbatar da labarin harin, inda ta ce a kokarin dakile harin ne ta harbe maharin inda shi ma ya mutu nan take.Harin na ba-zata, ya janyo rudani bayan tabbatar da mutuwar mutum hudu da suka hada da 'yan sanda uku da wani farar hula guda, amma kuma rundunar 'yan sandan ta nemi jama'a da su kwantar da hankulansu.

An dai karfafa tsaro a yankin da lamarin na wannan Laraban ya faru. Kawo yanzu ba a kai ga tantance ko harin na ta'addanci bane. Wannan ba shi bane karon farko da ake kai irin wannan harin a kasar ba, don ko a shekarar 1998, an kai wani harin ta'addanci a inda ofishin jakadancin Amirka ya ke, mutane da dama sun rasa rayukansu cikinsu har da ma'aikata na kasashen yamma da ke zaune a Tanzaniyan.