Hari akan sojojin NATO a Afghanistan
June 20, 2012Talla
Wani harin kunar bakin waken da aka kaiwa rundunar tsaron NATO a kudu maso gabashin kasar Afghanistan ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 11 yayin da da dama suka jikata.
Rahotani daga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP sun bayyana cewar maharin, ya tayar da nakiyar da ke dane a babur dinsa ne, a daidai lokacin da ya zo gab da wasu sojojin Naton da ke sintiri a wata unguwa ta garin Khost da ke yankin Gardez a jiya laraba,harin da kungiyar Alqa'ida ta daukin alhakin kaiwa.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umaru Aliyu