1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 25, 2018

Mutane da dama sun hallaka sakamakon harin da kungiyar IS ta kai a birnin Al-Suweida da ke kudancin kasar Siriya.

https://p.dw.com/p/325AU
Syrien Anschlag in Sweida
Harin kunar bakin wake a birnin Al-Sweida na SiriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/SANA

Kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin da Siriyan ke fama da shi, ta ce wasu mutane uku ne suka tayar da jigidar bama-bamai da ke jikinsu a garin na Al-Suweida. Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu kamar yadda kungiyar ta ruwaito, har da jami'an tsaro na gwamnatin Siriyan da kuma fararen hula. Kamfanin dillancin labaran Siriyan Sana ya ruwaito cewa kungiyar IS ta ce iat ke da alhakin kai harin.