1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a kusa da tashar makamashin nukiliya

Binta Aliyu Zurmi MAB
August 9, 2022

Akalla mutane uku sun rasa rayukansu yayin da wasu 23 suka samu munanan raunuka a ci-gaba da luguden wuta da Rasha ke yi a kusa da tashar makamashin nukiliya mafi girma a nahiyar Turai da ke kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4FK60
Ukraine I Zaporizhzhia I Saporischschja
Hoto: Dmytro Smolyenko/Ukrinform/IMAGO

Rahotannin da ofishin shugaban kasar Ukraine Volodmyr Zelensky ya fidda na nuni da cewar sama da rokoki 120 Rasha ta harba a kusa da tashar nukiliyar da ke kudancin kasar.

A yayin da Ukraine ke zargin Rasha da harba wadannan makamai, ita ma a nata bangaren Rasha na nuna wa ukraine yatsa. Wannan mataki  na kai hari a wannan tashar na nuna girman barazanar da ke tattare da fashewar makaman nukiliya wanda ke da matukar hadari.

Shugaba Volodmyr Zelensky na mai kira ga shugabannin kasashen yamma da su duba yiwuwar karin takunkuman da za su dakatar da Rasha a ci gaba da daukar irin wannan mataki.