1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An halaka mutane 50 iyaka da Chadi

Yusuf Bala Nayaya MNA
May 24, 2019

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa sama da mutane 50 ne suka rasu bayan wani hari da 'yan bundiga suka kai a wasu kauyika na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a kusa da iyaka da kasar Chadi.

https://p.dw.com/p/3IzqT
Zentralafrikanische Republik UN-Sicherheitstruppen in Bangui
Hoto: picture-alliance/AA/Stringer

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar bayan Allah wadarai da harin sun ce an baza ma'aikatan majalisar a wurin da lamarin ya faru.
Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yi gargadi ga kungiyar 3R mai dauke da makamai inda ta bukaci ta mika wadanda ke da hannu wajen harin da ya halaka mutanen.

Mai magana da yawun gwamnati Ange-Maxime Kazagui ya ce bayan wani hari da aka kashe wa kungiyar mutum guda ta rika kai hare-hare na ramuwar gayya. Ana dai zargin mayakan sakan da rashin mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla da shugabanni ciki kuwa har da yarjejeniyar da aka yi a watan Fabrairu.