1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe 'yan sanda hudu a Paris a cikin hari

Abdourahamane Hassane
October 3, 2019

Wani mutumin dauke da wuka ya kai hari a wani ofishin 'yan sanda na Paris, wani jami'in 'yan sanda ya ce mutum biyar suka mutu.

https://p.dw.com/p/3QgzT
Frankreich | Polizei | Messerangriff
Hoto: Reuters/P. Wojazer

 'Yan sandar sun bindige wanda ya kai harin, wanda daya daga cikin ma'aikatan hukumar 'yan sandar ne. Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron da ministan cikin gida Christophe Castaner sun  kai ziyarar gani da ido inda lamarin ya faru.