1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Ukraine sun karu a kasar Rasha

Mouhamadou Awal Balarabe
August 11, 2023

Sojojin Rasha sun zargi Ukraine da alhakkin harin da jirage marasa matuka suka kai a Moscow babban birnin kasar. Wannan dai shi ne karo na uku a ciki mako guda da ake harbo jirage marasa matuka a birnin Moscow.

https://p.dw.com/p/4V320
Daya daga cikin hari da aka kai da jirgi marasa matuki a birnin MoscowHoto: Ostorozhno Novosti/REUTERS

Rundunar sojojin Rasha ta sanar da cewa ta lalata wani jirgi marasa matuki mallakin Ukraine a yammacin birnin Moscow, lamarin da ke tabbatar da karuwar hare-haren da ake kaiwa babban birnin kasar. Cikin wani sako da ta wallafa a kafar sadarwa ta Telegram, ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta yi amfani da na'ura mai kwakwalwa wajen kakkabo wannan jirgi da ya fada wani daji ba tare da haddasa asarar rayuka ba.

Sai dai wasu filayen jiragen saman kasar sun dakatar da ayyukansu na wani dan lokaci a matsayin kandagarki kafin komai ya daidaita. Wannan dai shi ne karo na uku a ciki mako guda da ake harbo jirage marasa matuka a birnin Moscow. Ko da a karshen watan Yuli da farkon watan Agusta, an harbo jirage marasa matuka a yankin da ake hada-hadar kasuwanci a Moscow, lamarin da ya  barnata wasu sassa na gibe-gine guda biyu.