1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren NATO a Tripoli

June 25, 2011

Ƙungiyar tsaro ta NATO ta cigaba da lugudan wuta a birnin Tripoli a yayin da Majalisar Dattawan Amurika ta yi kira ga shugaba Obama ya janye sojojin Amurika daga Libiya

https://p.dw.com/p/11jZq
Hoto: picture alliance/dpa

Ƙungiyar tsaro ta NATo na cigaba da luggudan wuta a birnin Tripoli.An saurari fashewar wasu manyan bama-bamai cikin birnin.A cewar wakilin kamfanin dillancin Faransa AFP, bama-baman sun fashe a wata unguwa mai suna Tajura, inda NATO ke tsammancin akwai makaman sojojin Libiya jibge.

A ɗaya wajen, ƙungiyar tsaro ta NATO ta mussanta zargin da ake yi mata, na cewar hare-harenta, sun hallaka mutane 15 a Brega tsakanin jiya da yau.Su kuwa `yan tawayen Libiya, sun bada sanarwar cewar sun shiga tattanawa amma ba ta kai tsaye ba, da gwamnatin Libiya, inda suka bukaci shugaban Khaddafi ya sauka daga karagar mulki.

Majalisar Dattawan Amurika ta yi watsi da bukatar shugaban ƙasa Barack Obama, game da matsa ƙaimi wajen kai hare-haren a Libiya.Tare da gagaramin rinjaye ´yan majalisar Republican har ma da wasu na jam´iyar Democrate suka nuna adawa da wannan mataki.

Sun zargi shugaba Barack Obama da take dokokin ƙasa ta hanyar ƙaddamar da yaƙi a Libiya, ba tare da samun izini daga Majalisa ba.

A cikin wata wasiƙa da ya turawa ´yan Majalisar Amurika,shugaban ƙasar Libiya Mohamar Khaddafi ya yaba da halin dattakon da ya ce sun nuna.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Zainab Mohamed Abubakar