1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boma-bomai sun yi ajalin mutane a Najeriya

June 30, 2024

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da tashin wasu boma-bomai a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar, inda gomman fararen hulda suka rasa rayukansu.

https://p.dw.com/p/4hgdI
Hukumomin tsaro a wajen tashin Bom a jihar Borno a Najeriya
Hukumomin tsaro a wajen tashin Bom a jihar Borno a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/STR

Wasu hare-haren boma-bomai da aka kai wajen bikin aure da kuma wajen jana'iza a jihar Borno, sun salwantar da rayukan mutane da dama galibi mata da matasa da kuma kananan yara.

Lamarin ya faru ne a garin Gwoza da ke kudancin jihar, inda wasu ma fiye da mutum 100 suka jikkata.

Wadanda suka shaida lamarin da ya faru a jiya Asabar, sun ce bam na farko ya tashi ne a wurin bikin auren inda ake zargin wata matar da ta gabatar da kanta a matsayin mai bara ta tayar.

Na biyu kuma ya tashi ne a wajen da ake jana'izar daya daga cikin wadanda bam na farko ya hallaka.

'Yansanda sun ce mutum takwas ne suka mutu, amma wasu shaidun na cewa adadin ya zarta haka.