1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren kunar bakin wake sun hallaka mutane a Lebanan

Suleiman BabayoNovember 13, 2015

Hare-haren kunar bakin wake sun hallaka fiye da mutane 40 a yankin 'yan kungiyar Hezbollah na birnin Beirut fadar gwamnatin kasar Lebanan.

https://p.dw.com/p/1H4xi
Anschlag Beirut Libanon
Hoto: picture alliance/ZUMAPRESS/N.Lebanon

Fiye da mutane 40 suka hallaka yayin da wasu 240 suka jikata sakamakon hare-haren kunar bakin wake da suka ritsa da birnin Beirut fadar gwamnatin kasar Lebanon. An samu fashe-fashe mintoci tsakani a titin da ke da cinkoson shaguna cikin yankin da ke zama tungar kungiyar Hezbollah mai bin tafarkin Shi'a.

Tuni kungiyar IS mai neman kafa daular Islama ta dauki alhakin kai hare-hare, amma babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da labarin.

Kungiyar Hezbollah tana kan gaba wajen taimakon gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta Siriya da ke fuskantar kungiyoyi masu dauke da makamai da suka hada da kungiyar ta IS. Yakin basasan kasar ta Siriya na ci gaba sanadiyar mutuwar mutane da dama yayin da wasu mutanen ke ci gaba da gudun hijira.