1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare haren Jiragen yaƙi na ƙungiyar NATO a Libiya

April 12, 2011

Mayaƙan ƙungiyar NATO sun sake kai Farmaki akan wani garin da ke cikin hannu 'yan tawaye inda suka kashe fararan fula

https://p.dw.com/p/10rwN
Jiragen saman yaƙi na ƙungiyar NATO a samaniyar LibiyaHoto: AP

Jiragen saman na yaƙi na kungiyar tsaro ta NATO sun yi ruwan bama bamai a garin Kekla da ke a yankin Al jabal-Al-gharbi da ke cikin hannu yan' tawaye inda suka kashe wasu 'yan sanda da kuma faran fula.Gidan telbijan na kasar Libiya da ya bada labarin ya ambato cewar yawancin yan' sandar da ke a kan titin suna aikin bayar da hannu ga motocin da ke yin zirga zirga a garin sun mutu, yayin da kuma mata da yara ƙanƙana da dama suka rasa rayukansu a sakamakon harin

Wasu rahotannin kuma da ba a tabbatar da gaskiyar su ba na cewa dakarun gwamnatin na kanal Gaddafi sun kutsa a cikin garin da ke a cikin hannu yan' tawaye tun cikin watan afrilun da ya gabata.

A halin da ake ciki kuma tsohon ministan harkokin wajen ƙasar Libiya Moussa Koussa da ya yi marabus a cikin watan jiya ya samu izini daga hukumomin ƙasar Ingila inda ya ke gudun hijira domin hallarta taron da za yi na gaba akan Libiya a ƙasar Qatar.Wani kakakin ofishin ministan harkokin waje na ƙasar ta Britaniya da ya ce Koussa zai yi balaguron a ya ce zai bada gudun muwarsa a tattaunawar da za a yi .tun da farko dai a sanarwa da ya baiyana Mussa kousa ya yi gargadin cewa rikicin na Libiya na barazanar zamewa yaƙin basasa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman