1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren bama-bamai a Kadunan Najeriya

February 7, 2012

Mutane da dama sun jikata a kaduna da ke arewacin Najeriya bayan da wasu bama-bamai suka tashi a wasu sassa na birnin ciki kuwa har da wata cibiya ta sojoji.

https://p.dw.com/p/13ycM
Smoke rises from the police headquarters as people run for safety in Nigeria's northern city of Kano January 20, 2012. At least six people were killed in a string of bomb blasts on Friday in Nigeria's second city Kano and the authorities imposed a curfew across the city, which has been plagued by an insurgency led by the Islamist sect Boko Haram. There was no immediate claim of responsibility for the apparently coordinated attacks. REUTERS/Stringer (NIGERIA - Tags: CRIME LAW CIVIL UNREST TPX IMAGES OF THE DAY)IL UNREST)
Jihar Kano ma ta fiskanci hare-hare a ranar 20 ga janairu.Hoto: Reuters

A Najeriya wasu mutane da ba a tantance ko su wanene ba sun tayar da bama-bamai a wurare daban daban na birnin kaduna da ke arewacin ƙasar. Kakakin ƙungiyar agajin gaggawa ta ƙasa wato Yushua Shuaib ya bayyana wa kanfanin dillancin labarai na Reuters cewa mutane da dama ne suka jikata bayan tashin bama-bamai a kusa da wata cibiyar sojoji, da kuma kan babbar gadar da ke haɗa ɓangarori biyu na birnin na Kaduna.

Wannan harin ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ta ke fiskantar hare-haren bama-bamai daga ƙungiyar da aka fi sani da suna Boko Haram. Dama dai kuma birnin na Kaduna da ya ƙunshi mabiya manyan addinan ƙasar ya saba fiskantar rikice rikice na ƙabilanci da kuma na addini.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu