1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare sun halaka mutane 20 a Yemen

Mouhamadou Awal Balarabe
August 2, 2018

Wasu tagwayen hare-hare da ake zargin sojojin kawancen Yemen da kaiwa sun salwantar da rayukan mutane da dama a birnin Hodeidah, inda ake fama da rikici tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Huthi.

https://p.dw.com/p/32YEp
Jemen Kämpfe beim Flughafen Hodeidah
Hoto: Getty Images/AFP

Akalla mutane ashirin sun mutu yayin da dama suka jikkata a wannan Alhamis a birnin Hodeidah na Yemen, sakamakon wani harin jirgin sama da aka kai a wani asibiti da wata kasuwar sai da kifi. Kafofin watsa labarai da ke da kusanci da 'yan tawayen Huthi sun zargi gamayyar kasashen taron dangi da Saudiyya ke jagoranta da kai wadannan hare-haren guda biyu. Sai dai har yanzu fadar mulki ta Ryad ba ta ce uffan game da wannan batu ba.  

Tun a ranar 13 ga watan Yuni ne dakarun da ke biyeyya ga gwamnati Yemen tare da hadin gwiwar kawayenta na kasashen waje suka kaddamar da wani farmakin da nufin sake kwato birnin Hodeidah.  Ita dai matalauciyar kasar ta Yemen tana fama da rikici tun bayan da 'yan tawayen Huthi suka kama manyan sassa na kasar ciki har da sana'a babban birnin daga hannun gwamnatin shugaba Abd Rabbo Mansour Hadi.

Mutane kimanin dubu 10 suka mutu tun bayan barkewar yakin, yayin da miliyoyi kuma suka kaurace wa matsugunansu.