1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare hare a jihohin Gombe da Kano a Najeriya

February 25, 2012

An kashe mutane da dama a cikin hare haren bama baman da aka ɗora alhakin su akan ƙungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/149wj
A rescue worker inspects the burnt-out wreckage of cars and motorcycles destroyed by multiple explosions and armed assailants in the Marhaba area of the northern Nigerian city of Kano, on January 21, 2012. Coordinated bomb attacks on January 20 targeting security forces and gun battles have killed at least 121 people in Nigeria's second-largest city of Kano, with bodies littering the streets. AFP PHOTO / AMINU ABUBAKAR +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

An ba da rahoton cewar wasu 'yan bindiga sun kai wasu jerin munanan hare-hare a Gombe fadar gwamnatin Jihar da ke a yankin arewa maso gabashin Tarrayar Najeriya. An dai shafe sa'o'i da dama a daran jiya ana jin ƙarar fashewar abubuwan da kuma harbe-harben bindigogi abinda ya tilassawa mazauna birnin shige wa gidajen su.Tun daga misalin karfe bakwai da rabi na yammacin jiya ne aka fara jin tashin Bama-bama da kuma ƙarar bindigogi inda aka raba dare ana jin musayar wuta babu ƙaƙƙautawa.Hayaƙi ya turniƙe sama inda aka shaida ganin wuta na ci a babban Ofishin ‘yan sanda dake Gombe wanda kuma yake kusa da tudun hatsi da ke tsakiyar birnin.

Haka kuma rahotannin sun nuna cewa an kai hari a gidan yari sai dai babu cikakken bayani na irin ɓarna da aka yi a dukkanin wuraren.kawo yanzu.wakilin dw a Gombe ya ce har a safiyar yau an ci gaba da yin harbe harbe.Wannan dai shi ne karo na farko da al-ummar Gombe ke tsintar kan su a irin wannan munanan Hare-Hare .Gwamnatin jihar ta bakin Sakataren ta Abubakar Suke Bage ta sanar da dokar hana fita na tsawon awowi 24 har sai abinda hali ya yi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita .Mohammed Nasiru Awal