1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaMasar

Haramcin sanya nikabi a makarantun Masar

Mouhamadou Awal Balarabe
September 12, 2023

Ma'aikatar ilimi ta Masar ta haramta sanya nikabi a makarantun gwamnati da makarantu masu zaman kansu, matakin da ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta.

https://p.dw.com/p/4WFO6
Tsirarun 'yan mata da matan aure ne ke amfani da nikabi a Masar mai yawan MusulmiHoto: AP

A cikin sabuwar doka da jaridar gwamnatin Masar ta Akhbar al-Youm ta buga, fadar mulki ta Cairo ta kayyade kayan makaranta da daliban firamare da sakandare ya kamata su sanya tare da haramta rufe fuska. Sai dai 'yan Masar sun nunar da cewar hauhawar farashin litattafan da karancin guraben karatu da kayan aikin malamai ne ya kamata gwamnati ta maida hankali a kai maimakon haramta nikabi.

Karin bayaniMartani kan hana sanya Hijabi ko Nikabi

Duk da cewa galibin matan Masar na amfani da mayafi wajen lullube jikinsu, amma dai tsiraru ne ke amfani da nikabi a wannan kasa mai yawan Musulmi. Wasu daga cikin 'yan Masar sun fusata saboda gwamnati ba ta bayar da hujjar haramta nikabi ba, amma wasu sun danganta shi da matakin yaki da tasurin ra'ayin Islama.