1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na kira da a mutumta dimokuradiyya a Senegal

June 8, 2023

Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken, ya kira mahukuntan Senegal su mutunta dokokin dimokuradiyya yayin da kasar ta fada kazamin tashin hankali mai nasaba da rikicin siyasa.

https://p.dw.com/p/4SLag
Hoto: JEROEN JUMELET/ANP/picture alliance

Babban jami'in diflomasiyyar na Amirka ya kira shugaba Macky Sall a wannan Laraba ta wayar tarho domin jan hankalinsa kan tarzomar da ta barke a kasar a lokacin da kotu ta yanke wa madugun adawa Ousman Sonko hukuncin daurin shekaru biyu a gidan kaso bisa zarginsa da cin hanci da kuma aikata fyade.

Blinken ya kuma mika ta'aziya da suna gwamnatin Amirka ga shugaba Sall kan mutuwar mutane 16 da aka samu a yayin boren nuna bacin rai da ya barke ranar da aka yankewa Sonko hukuncin da ka iya hana masa tsayawa takara a zabukan kasar da ke tafe a shekarar 2024.

Bayan tattaunawar, Blinken ya jaddada goyon bayan Amirka ga al'ummar kasar Senegal a cikin wani sakon tweetter da ya wallafa.