Hankula sun kwanta a Thailand
July 18, 2018Talla
A wannan Larabar ce yaran nan 'yan kwallon kafa na kasar Thailand tare da kocinsu da aka ceto a kwanakin baya, daga wani kogo, sun yi bayyanarsu ta farko.
Sanye da rigunan wasanni masu launin fari da kore, an nuno su cikin annashuwa a wannan Larabar, a birnin Chiang Rai na kasar ta Thailand.
Yaran su 12 da kocin na su, sun fito bainar jama'a ne lokacin wani taron manema labarai, mako guda bayan nasarar kubutar da su da wasu gwanayen nutso suka yi.
Tun bayan ceto su da aka yin dai sun kasance karkashin kulawar likitoci da masana halayyar dan Adam, wadanda suka tabbatar da sun dawo hayyacinsu, saboda tsananin tashin hankali da suka yi fama da shi.