1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shirya zaman taron kawar da makaman nukiliya

Ramatu Garba Baba ATB
June 10, 2018

Hankula sun karkata kan kasar Singapore, bayan da shugaban kasar Amirka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa suka isa kasar domin halartan taro a kan shirin kawar da makaman nukiliya daga yankin tsibirin Koriya.

https://p.dw.com/p/2zFQa
Friedensnobelpreis 2017 ICAN
Hoto: PAX

Wannan shi ne karon farko da shugaban Koriya ta Arewa ya amince ya tattauna kai tsaye da shugaban wata kasa ta yammacin duniya domin a tattauna kan shirin mallakar makamin nukiliya da ya sa a gaba. Daman a jibi Talata ranar sha biyu ga wannan watan na Yuni aka tsara yin zaman da ake ganin zai kawo karshen takaddama a tsakanin Koriya ta Arewan da wasu kasashen yamma da ke baiyana fargabar kan barazanar da nukiliyar ke yi ga zaman lafiyar al'ummar duniya baki daya.