1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Hamilton Naki: Mai basirar kirkira karkashin mulkin wariya

October 18, 2020

Da ilimin zamani kalilan karkashin gwamnatin nuna wariyar launin fata, Hamilton Naki ya tashi da mai kula da furenni zuwa babban mai kula da dakin bincike da ake girmamawa.

https://p.dw.com/p/3k6qQ
Projekt African Roots | Hamilton Naki - Porträt

A ina aka haifi Hamilton Naki?

Mai yuwuwa an haifi Hamilton Naki a shekarar 1926 a kauyen Centane na Afirka ta Kudu (a largin gabashin kasar na yanzu). Tun da yake iyayensa talakawa ne, haka ya tilasta masa neman abin yi tun yana karami. Hamilton Naki yana da mata da yara hudu maza, gami da 'ya mace daya. Ya mutu sakamakon bugun zuciya ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2005.

Mene ne aikin Hamilton Naki na farko?

Yana da shekaru 14 bayan kammala makarantar firamari, Naki ya tafi neman aiki a birnin Cape Town. Ya samu aiki da Jami'ar Cape Town a matsayin mai kula da furenni. Ya zama mai kula da wajen Wasan Tennis na jami'ar.

Yaya aikin Hamilton Naki ya kasance?

Har zuwa shekarar 1954, ya kasance a dakin binciken dabbobi. A wannan lokacin ne masanin zuciya da ke bincike Dr. Robert Goetz na gano Naki yana da wata fasaha ta musamman. Ya koya masa yadda ake gyara dabbobin domin yi musu fida. Daga bisani Naki ya zama mai kula da wajen binciken na makarantar horas da likitoci. Ya kuma koyi yadda ake yi wa dabbobin dashen bangaren jiki a dakin bincike. Wannan ya saka ya yi aiki da Farfesa Christiaan Barnard likitan zuciya na farko wanda ya fara dashen zuciyar dan Adam.

Shin Hamilton Naki ya taba dashen bangaren jikin mutum?

Projekt African Roots | Hamilton Naki

A'a, bai taba ba. Naki ya yi aiki lokacin mulkin nuna wariyar launin fata. A matsayinsa na bako ba shi da wata dama ta aiki domin Turawa ne kadai suke yin aikin fida. A gaskiya, dokokin sun haramta wa ma'aikatan lafiya bakaken fata kula da marasa lafiya Turawa. Naki ya ba da taimako kan shirye-shirye da kuma bincike na yanayin fida.

Shin Hamilton Naki ya taimaka a dashen zuciya na farko?

Hamilton Naki ba ya nan a lokacin da a ranar 3 ga watan Disamba 1967, tawagar masi aikin fida karkashin Christiaan Barnard suka cire zuciyar mamaci Denise Darvall wanda ya amince domin dasawa ga Louis Washkansky.

Dakin kula da tarihin zuciya na Cape Town wanda aka gina domin girmama mutanen da suka taka muhimmiyar rawa a dashen zuciyar ta ce aikin Naki tare da Chris Barnard na fara allurar kashe zafin ciwo kan dabbobi. Naki ya nuna bujinta tare da samun daukaka har zuwa matsayin babban mai kula da dakin bincike. A cikin wani rubutun majallar jami'ar horas da likitoci ta Ingila a shekara ta 2014 an rubuta cewa "Naki ya taimaka kan allurarar kashe zafin da aka yi wa kare domin samun mafita kan cutar zuciya." Haka ya nuna yana cikin tawogar da ta samar da hanya da nasarar aikin da Barnard ya samu.

Majiyoyi da dama sun ce Hamilton Naki na cikin wadanda suka fara dashen zuciya. Me ya janyo jita-jitar?

Karkashin tsarin wariyar launin fata ana dakile nasarorin da bakaken fata masu rinjaye suka samu, sabuwar Afirka ta Kudu tana da burin sauya wannan rashin adalcin. Aikin Naki na cikin irin labaran da bakaken fata masu yawa suka fuskanta a Afirka ta Kudu. Bayan mutuwar Hamilton Naki ranar 29 ga watan Mayu 2005 ,an wallafa rubuce-rubuce masu yawa da suka hada da cewa yana cikin wadanda suka fara aikin dashen zuciya ga dan Adam. Daga bisani an sake wannan rubutun domin janye maganar. A shekara ta 2009 cikin wani shirin mai suna "Boyayyar Zuciya" an nuna cewa mai yuwuwa an dakile irin rawar Naki ya taka. A cikin shekarun da suka gabata iyalansa sun nuna irin wannan tunanin. Daya daga cikin 'ya'yansa mai suna Thembinkosi Naki ya ce mahaifinsa ne ya yi aikin. Sannan ya kara da cewa "Abin da ya bata masa rai matuka. Chris ya samu duk kyautukan, amma babana bai samu komai ba."

Yaya Christiaan Barnard yake ji game da gudumawar Hamilton Naki?

Projekt African Roots | Hamilton Naki

Bayan shekaru da aikin Christiaan Barnard ya yi magana kan yadda yake girmama Hamilton Naki. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na AP a shekarar 1993 ya ce "Idan Hamilton ya samu damar zai yi, zai iya zama likitan da yake da matukar basira." A shekar ta 2001 kafin mutuwarsa, ya sahida wa jaridar Birtaniya ta Daily Telegraph cewa Naki ya zama "daya daga cikin manyan masu bincike a bangaren dashen zuciya... Yana da sani musamman kan yin abubuwa da sarrafawa da hannu sosai."

Shin Hamilton Naki ya samu kyautar yabo?

A shekara ta 2002 tsohon shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki ya ba da kyautar girmamawa ta kasa ga Hamilton Naki wanda ake bai wa ga 'yan Afirka ta Kudu da suka nasara matuka. A shekara ta 2003 ya samu kyautar girmamawa daga bangaren likitoci na Jami'ar Cape Town.

Yaya sunan Hamilton Naki ya ci gaba?

A shekara ta 2007 an kaddamar da ba da gurbin karatu na Hamilton Naki.  Likitocin da suka nuna sha'awa da aikin Naki suke ba da tallafin karatun ga 'yan Afirka ta Kudu marasa galihu a bangaren bincike. A lokaci guda Gidauniyar Kula da Bincike ta kasa tana ba da kyauta mai suna Hamilton Naki ga mutanen da suka yi fice da nuna bajinta a bincike duk da kalubalen da suka fuskanta. A shekara ta 2017 an sakawa wajen shakatawar jama'a da ke birnin Cape Town sunan Hamilton Naki wanda yake daura da asibitin Christiaan Barnard.