Hamas ta sako sojoji hudu na Isra'ila
January 25, 2025Kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta sako mata sojojin Isra'ila guda a wani bangare na cika yarjejeniyartsagaita wutarda suka cimma kan yakin da aka dauki watanni ana gwabzawa a Zirin Gaza.
Sojojin na Isra'ila dai sun fito cikin alamu na koshin lafiya, suna daga cikin mutane 251 da Hamas ta yi garkuwa da su a harin da ta kai wa Isra'ila a ranar 07 ga watan Oktobar 2023. Akwai wata soja guda daya da rahotanni suka ce tana hannun kungiyar Hamas amma za su sako ta a makonnin da ke tafe.
Musayar mutanen na cikin bangaren yarjejeniyar tsagaita wuta wadda mutane kefargabar dorewartada ta fara aiki a ranar Lahadin da ta gabata. Kasashen Qatar da Amurka sun sanar da ita kwanaki gabanin karbar mulkin Donald Trump a Amurka, amma tuni ya yi ikirarin cewa shi ne ya assasa samar datsagaita wutar bayan an kwashe watanni ba tare da cimma matsaya a kanta ba.