1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ilar ta kubutar da wani sojanta guda daga Hamas

October 30, 2023

Isra'ilar ta kubutar da wani sojanta guda daya daga hannun Hamas bayan farmaki ta kasa da ta kai Gaza.

https://p.dw.com/p/4YDHs
Hoto: Dan Kitwood/Getty Images

Kungiyar Hamas ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna wasu mata 3 'yan Isra'ila da ta yi garkuwa da su, wadanda suka zargi firaministan Isra'ilar Benjamin Netanyahu da gaza kare su.

Daya daga cikin matan mai suna Danielle Aloni wadda ta yi jawabi, ta yi kira ga Netanyahu da ya nemi tattaunawa da Hamas don ganin an sako su ta hanyar musayar fursunoni.

Karin bayaniYakin Gaza ya hallaka mata da kanana yara kusan dubu shida

Da almurun nan ne dai iyalan matan za su gana da 'yan jarida kan batun, inda shi kuma Netanyahu ya jaddada kudurinsa na ganin ya kubutar da dukkan mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, tun bayan barkewar yakin Isra'ila da Falasdinawa a zirin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban nan da ke dab da kare wa.

Tuni dai rundunar sojin Isra'ilar ta sanar da kubutar da wani sojanta guda daya daga hannun Hamas, bayan farmaki ta kasa da suka kai Gaza.