1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da Sudan ta Kudu ke ciki shekara guda bayan samun 'yancin kai.

July 9, 2012

Duk da albarkatun man fetur da Sudan ta Kudu ta mallaka,talauci da rashin tsaro sun mamaye al'umar ƙasar shekara guda bayan samun 'yancin kai daga Sudan

https://p.dw.com/p/15U1G
Am 9.7.2011 wird Südsudan ein unabhängiger Staat.

A wannan Litinin Tara ga watan Juli aka cika shekara guda da samun 'yancin kan ƙasar Sudan ta Kudu, sai dai kuma yayin da a baya kafofin yaɗa labarai na duniya suka maida hankali wajen yin tsokaci akan rikicin kan iyaka tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, a waje guda kuma sun manta da rikicin cikin gida na Sudan ta Kudu. A farkon wannan shekarar dai mutane fiye da 900 ne aka kashe a rigingimun ƙabilanci a ƙasar wanda kafofin yaɗa labarai su ka ruwaito yawaitar harbe-harbe da kuma fashi da makami.

Rigingimun na Kudancin Sudan dai sun samo asali ne daga tsawon shekaru na yaƙin basasar da aka yi ta fama da shi a yankin. Dubban ƙananan makamai sun yaɗu a hannun jama'a, a waje guda kuma ga matsalar talauci inda tsoffin sojojin ba sa samun kuɗin shiga sannan a ɗaya ɓangaren ga ƙungiyoyin 'yan tawaye masu ɗauke da makamai, dukkan waɗannan matsaloli sun tattaru wajen haifar da rikici a yankuna da dama na Sudan ta Kudu matsalolin kuma da suka gagari jami'an tsaro wajen bada kariya ga rayuwar jama'a.

Babu dai wanda ke inkarin ƙwarewar Yuang Makette shugaban 'yan sanda na Juba babban birnin ƙasar, sai dai a waje guda babbar matsalar da yake fuskanta ita ce rashin kayan aiki:

Ya ce ina bukatar mota don ɗaukar masu laifi waɗanda mu ka tsare a Chaji ofis na wucin gadi, domin kai su gidan yari, a yanzu haka sai na yi hayar motar, saboda haka muna bukatar mota da babur ga jami'ai na domin gudanar da aikin bincike.

Southern Sudanese celebrate independence from northern Sudan at midnight in Juba, Saturday, July 9, 2011. South Sudan became the world's newest nation early Saturday, officially breaking away from Sudan after two civil wars over five decades that cost the lives of millions. (Foto:Pete Muller/AP/dapd)
Bikin samun 'yanciHoto: dapd

Tsawon shekaru 25 cur Yuang Makette ya kwashe yana aiki a rundunar sojin Sudan, inda ya kai ga muƙamin Kanar. Kana daga bisani ya sami ƙarin horo ya kuma zama shugaban 'yan sanda. Yawancin manyan jami'an 'yan sandan dai suna kuma da horon soji:

Yace a da, mun yiwa wata ƙasa yaƙi domin tabbatar da tsaro kuma akan makamancin wannan dalili ne a yau na ke aikin ɗan sanda. Aikin ɗan sanda yana da muhimmanci ƙwarai saboda ana yi ne domin tsaron lafiyar al'umma."

Ba kasafai dai al'amura ke tafiya salin alin a ƙasar ta Sudan ta Kudu ba. A farkon wannan shekarar mutane fiye da 900 ne suka rasa rayukansu a rikicin kabilanci tsakanin kabilar Nuer da Murle arewa maso gabashin ƙasar. Babu dai 'yan sandan da za iya kwantar da wannan tarzoma a cewar Wolf Christian Paes masani kan harkokin Sudan a cibiyar bincike ta BICC dake nan Bonn:

Ya ce a wannan yanki inda satar dabbobi ya zama babbar matsala, 'yan sanda ƙalilan ne ke akwai kuma ma basu da abin hawa basu da naurorin sadarwa a saboda haka suna cikin halin tsaka mai wuya da ba za su iya bada cikakken tsaro da kariya ba a faɗin wannan yanki.

Sai dai kuma ba wannan ce kaɗai matsalar da ta addabi yankin ba, wadda ya yi fama da yaƙin basasa, akwai yaɗuwar ƙananan makamai a ko ina. Makamai fiye da 700,000 ne aka ƙiyasta su ke hannun jama'a. Gwamnati ta sha yin ƙoƙarin karɓe makaman amma kuma lamarin yaci tura, kamar yadda Wolf Christian Paes ya nunar:

BRUSSELS, March 20, 2012 President of South Sudan Salva Kiir Mayardit speaks during a press briefing after meeting with President of European Commission Jose Manuel Barroso (not seen) at the EU headquarters in Brussels, capital of Belgium, March 20, 2012
Salva Kiir Mayardit shugaban Sudan ta KuduHoto: picture alliance / ZUMA Press

Ya ce ba zai wadatar ba a karɓe makamai daga hannun wata ƙungiyar ƙabila, wajibi ne a kwance ɗamarar sauran ƙungiyoyi dake kan tsaunuka ko kuma a maƙwabtan ƙasashe. Wannan shine abin da ya gaza samuwa, domin idan an ɗinke ɓaraka ɗaya ta karɓe makamai, bayan makwanni ko 'yan watanni sai kuma ka ji wata sabuwa ta ɓullo ta satar dabbobi dama kuma tara makamai.

A yanzu dai ana iya cewa akwai alamu masu ƙarfafa gwiwa cewa gwamnatin Sudan ta Kudu ta ƙaddamar da shirin yin garanbawul ga rundunar 'yan sanda. Akwai bukatar a baiwa jami'an 'yan sandan cikakken horo, bugu da ƙari akwai bukatar ƙasashe masu bada agaji su taimaka musu da kayan aiki, hakan na kuma, ya kamata a hanzarta aiwatar da kashi na biyu na shirin shigar da tsoffin 'yan tawayen cikin al'amuran ƙasa. Ba dai abu ne mai sauki ba, domin zai ɗauki lokaci kafin a gyara ta'adin da yaƙin basasa da aka kwashe shekaru 50 ana yi ya haifar.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi