Haiti: Rantsar sabuwar gwamnatin rikon kwarya
April 25, 2024Talla
Za a gudanar da bikin rantsar da sabuwar gwamnatin rikon kwarya a Haiti a offishin Firanministan kasar inda ake sa ran gwamnatin mai mambobi 9 ta cike gibin shugabancin kasar. Kasar ta Haiti dai ta fada cikin rikicin siyasa ne bayan da kungiyoyin miyagu suka far wa babban birnin kasar Port-au-prince tare da mika bukata ga Firanminista Ariel Henry da ya yi murabus.
Karin bayani: Jagororin siyasar Haiti sun amince da kafa gwamnatin rikon kwarya
Ana dai ganin akwai jan aiki a gaban sabuwar gwamnatin rikon kwaryar ciki kuwa har da shirya babban zabe a watan Fabarairun 2026 a kasar da rabon da ta shirya zabe tun a shekarar 2016.